[… Franklin Bulls ke riƙe da ƙwallo a halin yanzu kuma kai-tsaye Payton Hughes sun sami ƙwallo kuma sun miƙa ta zuwa Kendry Rams wanda ke neman kutsawa cikin hanzari sannan tsaye a wurin wani matashi ne mai jini a jika wato Tom Isaac wanda shi wannan Tom Isaac kwata-kwata kamar babu mai tsaronsa a cikin wannan wasa kamar yana jiran wata dama ce ta zo kamar dai babu wanda yake tsare shi kawai dai suna wani salon wasa ne wanda zai ba su damar zura ƙwallo, kawai dai sun bar shi a gefe domin samun dama ta samun nasara to amma su kuma Bulls sun gane wannan wayon saboda haka basu ba da wata dama ba ta barin samun nasara ta amfani da wannan salo. E Isaac, wannan hange ne mai kyau domin bakiɗayan wannan salo na tsaro ya tattara ne a wannan ɓangaren filin wasan inda yake sa ran cin ƙwallo ɗaya mai maki uku ta hanyar jifan haɗa baya-da-baya wanda zai yi wahala ya sami haka. To amma Martin kana jin cewa su ma za su sami damar kai wa zuwa bakin raga? Dama ta biyu ta sake samuwa ga Rams wanda kamar ba ya cikin wasan. Ban taɓa ganin abun ban sha’awa irin wannan ba daga Rams a wasan ƙwallon Kwando. Abun akwai burgewa …]  | Entry #38944 — Discuss 0 — Variant: Kanokanoo
| Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
|---|
5 | 1 x4 | 0 | 1 x1 |
|
[… zai zama Franklin Bulls da riƙon farko sai nan Payton Hughes ya sami ƙwallon don miƙa shi wa Kendry Rams yana jifar da wuri da neman birki da sauri sai nan ga matashi Tom Isaac Tom Isaac ba ya nan ma a riƙon ƙariya a wannan wasan kawai yana ɗiban abinda ke akwai ne ba ya ma wasan ƙariya kawai suna wasan yanki na a ne yanki mai muraba'i kuma yana barinsa a waje kuma zasu yi Hail Mary amma Bulls sun dawo kan lokaci babu dama domin Hail Mary akan wannan dabarar mai jan hankali eh hange mai jan hankali sosai Isaac cikin dukkan wannan masu kariya suna nan a wannan gefe na filin zaya abka wajen neman maki uku ya nemi bugun baya da baya ba zasu same shi ba ko za su sami allon hari shi ma Martin babbar damar bugu na biyu ga Rams kuma ba ya cikin wasan ban taba ganin wani abu kamar wannan ba a wasan ƙwallon kwando abin ban mamaki daga Rams ya zame wani baƙon abu …] | Entry #38621 — Discuss 0 — Variant: Not specifiednone
| Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
|---|
2 | 0 | 1 x2 | 0 |
|
Kungiyar Franklin Bulls ne zasu fara a wasan, Kai tsaye Payton Hughes ne ya karbi kwallon inda ya ke neman yadda zasu saka kwallon a ragar Kendry Rams da wuri-wuri, ya hango Tom Isaac Wanda ba ya cikin Yan baya a wasan, ya na ta lalube ne kawai yadda ya zama a gefe don satar numfashinsu, amma sai yan Bulls din su ka yi hanzarin dawowa don toshe wannan damar, abin sha'awa kariya ce Mai kyau haka nan abin burgewa a duk wannan lokaci Isaac na ta wannan bangare a kokarinsa na saka kwallo Mai maki uku, a jere amma Hakan Bai samu ba, zasu iya Kai hari kuwa, gagarumar dama ga Martins na Bulls ya saka kwallon a raga amma ba a bashi kwallon ba, ban taba ganin irin wannan ba, wasan kwallon kwando Mai matukar kayatarwa daga bangaren Rams...abin da mamaki | Entry #38767 — Discuss 0 — Variant: Kanokanoo
| Voting points | 1st | 2nd | 3rd |
|---|
2 | 0 | 1 x2 | 0 |
|